IQNA

Gwamnatin Da Za A Kafa Iraki Za Ta Yi Bincike Kan Kisan Sulaimani

23:59 - April 24, 2020
Lambar Labari: 3484742
Tehran (IQNA) Mustafa Alkazimi firai ministan da aka dorawa alhakin kafa sabuwar gwamnati a Iraki ya sha alwashin gudanar da bincike kan kisan Sulaimani da Muhandis.

Tashar Almauadeen ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da kungiyar Hizbullah a Iraki ta fitar, ta tabbatar da cewa, a zaman da mambobinta suka gudanar da Mustafa Alkazimi, ya tabbatar musu da cewa zai kafa kwamiti wanda zai gudanar da bincike kan kisan gillar da aka yi wa Qasim Sulaimani da Abu Mahdi Al-Muhandis.

A cikin bayanin nasa Kazimi ya jaddada cewa, wannan ba batu ne wanda za a yi shiru a kansa ba, domin kuwa babban lafi aka aikata, kuma dole a gano yadda lamarin ya faru da kuma masu hannu a cikin shirya hakan, domin su fuskanci hukunci na adalci.

Kungiyar Hizbullah Iraki ta bukaci da a rika bayar da bayanin sakamakon binciken daki-daki ga al’ummar Iraki, domin su san halin da ake ciki kan batun.

 

3893719

 

captcha