IQNA

Nasihar Taruti Ga Makaranta Kur’ani A Masar

15:55 - May 06, 2020
1
Lambar Labari: 3484767
Tehran (IQNA) Abdulfattah Taruti fitaccen makarancin kur’ani mai tsarki dan kasar Masar ya yi nasohohi ga makaranta kur’ani.

Shafin yada labarai na sadal balad ya bayar da rahoton cewa, a cikin wannan yanayi na yaduwar cutar cortona a kasar Masar, wada yasa makaranta basa halartar tarukan karatu, akwai abubuwa da ya kamata su rika yi.

Ya ce duk da rashin halartar wuraren tarukan a cikin watan Ramadan, dole ne makarancin kur’ani ya yawaita tilawa a duk inda a cikin gidansa ne ko  awani wuri na daban, domin kada sautinsa ya dushe.

Haka nan kuma yin amfani da tsari wajen yin karatun, ta yadda idan zai yiwu mutane su amfana ko da hanyoyin sadarwa ne na zumunta.

Ya ce akwai lokutan da yake halartar wuraren karatun kur’ani a cikin hunturun sanyi, kuma yana tafiya mai nisa kafin ya isa wurin, amma saboda ya cimma manufarsa ta yada kur’ani ya kan daure domin yin hakan.

Kamar yadda yay i nasiha ga makaranta kan su rika yin amfani da sautuka daban-daban da salo daban-daban domin kayata karatunsu da kuma kyautata karatun ayoyin ubangiji.

Taruti yana yin karatun kur’ani da salon malamai irin sheikh Muistafa Isma’il, Shuhat Anwar, Muhammad Siddiq Minshawi, Mustafa Galwash da makamantansu.

 

3896588

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: Taruti nasihohin
Wanda Aka Watsa: 1
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
aliyu musa
0
0
ina so wannan sako
captcha