IQNA

EU Ta Yi Barazanar Kakaba Ma Isra’ila Takunkumi Kan Mamayar Yankunan Falastinawa

23:53 - May 11, 2020
Lambar Labari: 3484787
Tehran (IQNA) kungiyar tarayyar turai ta yi barazanar kakaba wa Isra’ila takunkumi matukar ta aiwatar da shirinta na hade yankunan Falastinawa da ke gabar yamma da kogin Jordan.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, kakakin kungiyar tarayyar turai Peter Stano ya bayyana cewa, idan har Isra’ila ta ci gaba da mamaye yankunan Falastinawa musamman shirin hade yankunan gabar yamma da kogin Jordan, to tarayyar turai za ta dauki mataki.

Ya bayyana hakan ne a lokacin taron manema labarai na kwamitin zartarwa na kungiyar tayarraui, inda ya ce hade yankunan Falastinawa na gabar yamma da kogin da yankunan Isra’ila, ya sabawa dukkanin dokoki na duniya.

Ya ce idan har Isra’ila ta aiwatar da wannan shiri nata, to kungiyar tarayyar turai za ta dauki matakin da ya dace kan hakan, na yin mu’amala da shirin a  matsayin wanda ya saba wa dokokin duniya.

Kamfanin dillancin labaran WAFA ya bayar da rahoton cewa, a ranar Juma’a mai zuwa ministocin harkokin waje na kungiyar tarayyar turai za su gudanar da zama kan wannan batu.

Wannan shiri na Isra’ila na zuwa ne bayan samun lasisin yin haka daga gwamnatin Amurka kai tsaye, lamarin da ke ci gaba da fuskantar kakkausar suka daga al’ummomin duniya.

 

 

3898217

 

Abubuwan Da Ya Shafa: amurka gwamnati
captcha