Wannan masallacin a wurin mabiya mazhabar ahlul bait (AS) yana a matsayin masallaci na hudu wajen dara bayan masallacin Ka’abah, masallacin ma’aiki (SAW) da kuam masallacin Aqsa. Shi ne masallacin Amirul Muminin Ali Bin Abu Talib (AS) kuma a ickin wannan masallaci Abdulrahman Bil Muljam ya sare shi da takobi har ya yi shahada.