IQNA

An hana Yawon Gaisuwar Salla A bana a kasar Aljeriya

23:01 - May 17, 2020
Lambar Labari: 3484808
Tehran (IQNA) ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Aljeriya ta sanar da wajabcin dakatar da duk wasu harkokin kai komo a ranar salla.

Kamfanin dillancin labaran anatoli ya bayar ad rahoton cewa, ministan ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar ajeriya ya sanar da cewa, bisa la'akari da halin da ake ciki na yaduwar cutar corona, an dakatar da duk wasu harkoki na gaisuwar salla a tsakaknin al'umma kai tsaye.

Ya ce za a iya gudanar da irin wadannan harkoki da aka saba a kowace amma ta hanyar hanyoyin sadrawa  awannan shekara-shekara, amma babu tafiye-tafiye.

shi ma  anasa bangaren ministan kiwon lafiya na kasar ta Aljeriya ya ce suna yin kira ga mutane da su guji yin tafiye-tafiye ad haduwa da dangi da 'yan uwa da abokan arziki kamar yadda aka saba yia  ranar salla.

Kasar Aljeriya yanzu dai yana da mutane 6629 da suka kamu da Corona, 536 sun riga mu gidan gaskiya.

3899392

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kasar aljeriya sallar idin bana
captcha