IQNA

Dakarun Haftar Sun Sanar Da Tsagaita Wuta A Libya

22:45 - May 20, 2020
Lambar Labari: 3484819
Tehran (IQNA) Dakarun da ke biyayya Khalifa Haftar a kasar Libya sun sanar da tsagaita wuta a cikin wannan mako.

Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da ya fitar, mai magana da yawun dakarun Haftar Janar Ahmad Almismari ya bayyana cewa, daga yau Laraba za su tsagaita bude wuta, kuma za su janye dakarunsu kilomita 2 zuwa 3 daga gefen birnin Tripoli.

Ya ce sun dauki wannan matakin ne saboda wannan shi ne mako na karshe na watan Ramadan, kuma jama’a suna bukatar gudanr da hada-hadar sallar idin fitr, domin jama’a su gudanar da harkokinsu cikin natsuwa, hakan yasa suka dauki wannan mataki.

Janar lmismari ya kara da cewa, tun daga farkon watan Ramadan mai alfarma suka sanar da dakatar bude wuta tsawon watan na Ramadan, amma gwamnatin Tripoli ta yi watsi da hakan, inda ta ci gaba da kai hare-hare a cikin watan, wanda hakan yasa ala tilas su ma suka dauki irin wanann mataki.

Dakarun haftar na zargin Turkiya da kwaso dubban ‘yan ta’adda daga Syria zuwa Tripoli, domin yaki da dakarun na Haftar, kamar yadda Majalisar dinkin duniya ma ta tabbatar da cewa, an kwaso dubban ‘yan ta’adda daga Syria zuwa birnin Tripoli.

3900302

 

captcha