IQNA

Ayatollah Ozma Sayyid Ali Khamenei

Al'ummar Falastinu Suna Cikin Fadaka Kuma Suna Kara Fadaka Fiye Da Kowane Lokaci

14:49 - May 22, 2020
Lambar Labari: 3484823
Tehran (IQNA) Jagoran juyin juya halin musulunci a Iran ya gabatar da jawabin ranar Quds ta duniya a yau Juma'ar karshe ta watan ramadan. Ga dai matanin jawabin

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammadu da Alayensa tsarkaka da zaɓaɓɓun sahabbansa da mabiyansu har zuwa tashin ƙiyama.

Ina miƙa gaisuwa da sallama ga dukkanin 'yan'uwa musulmi maza da mata a duk faɗin duniya, sannan ina roƙon Allah Maɗaukakin Sarki da Ya karɓi ibadunsu a watan Ramalana mai albarka. Haka nan ina isar da saƙon taya murnar ƙaramar salla a gare su, kamar yadda kuma ina gode wa Allah Ma'abocin karimci saboda ni'imar da yayi mana na kasantuwa cikin wannan wata na baƙuncin Ubangiji.

Yau ranar Ƙudus ce; ranar da bisa hikima da hangen nesan Imam Khumaini aka ƙirƙiro ta a matsayin wata kafa ta tattaro muryoyin musulman duniya waje guda don goyon bayan Ƙudus mai alfarma da kuma Palasɗinu da ake zalunta. Tsawon waɗannan gomomin shekaru ta taka gagarumar rawa sannan a nan gaba ma za ta taka insha Allah. Al'ummomi sun karɓi Ranar Ƙudus hannun bibbiyu, sannan kuma har yanzu suna ganin hakan a matsayin wani aikin wajibi da ke wuyansu na ci gaba da riƙo da tafarkin 'yancin Palasɗinu da kuma girmama hakan. Babbar siyasar ma'abota girman kai da kuma sahyoniyawan duniya ita ce rage kaifin lamarin Palasɗinu da kuma cire shi daga ƙwaƙwalan al'ummar musulmi don a manta da shi. Nauyi na gaggawa da ke wuyanmu shi ne faɗa da wannan ha'incin da 'yan amshin shatan maƙiya suke yi a fagagen siyasa da al'adu a waɗannan ƙasashe na musulmi. Sannan kuma haƙiƙanin lamarin shi ne cewa lamari mai girman gaske kamar lamarin Palasɗinu ba lamari ne da kishi, dogaro da kai da kuma irin sanin ya kamatan da al'ummar musulmi suke ci gaba da samu zai bari a mance da shi ba, ko da kuwa Amurka da sauran 'yan mulkin mallaka da 'yan koransu na yankin nan sun yi amfani da kuɗi da kuma dukkanin ƙarfin da suke da shi.

Batu na farko shi ne tunatarwa dangane da girman wannan lamari na fashin ƙasar Palasɗinu da kuma kafa tushen cutar kansa ta sahyoniyawa (Isra’ila) a wajen da aka yi. Daga cikin ayyukan Allah wadai na bil'adama cikin wannan zamani da muke ciki, babu wani mummunan aiki da ya kai wannan girma da muni. Fashin wata ƙasa da kuma korar mutanen cikinta har abada daga gidaje da kuma ƙasar iyaye da kakanninsu, shi ɗin ma da irin wannan mafi munin na'uoi na kisa da ta'addanci da lalata ‘shuka da iri’ da kuma ci gaba da wannan zalunci tsawon shekaru aru-aru, ko shakka babu hakan wani sabon rakodi ne aka kafa cikin shaiɗana da ashararancin bil'adama.

Manyan masu laifi cikin wannan ɗanyen aikin su ne gwamnatocin ƙasashen yammaci da siyasarsu ta shaiɗanci. A wancan lokacin da gwamnatocin da suka yi nasara a yaƙin duniya na ɗaya, suka ɗauki tushen yankin Yammacin Asiya wato gwamnatin Usumaniyya a matsayin babbar ganimar yaƙi da kuma yin watandarta a tsakaninsu a taron da suka gudanar a birnin Paris, sun ji cewa lalle suna buƙatar wani sansani na tsaro a tsakiyar wannan yanki da zai lamunce musu iko da kuma mulkinsu na dindindin a yankin. Shekaru aru-aru kafin hakan, Ingila ta hanyar ‘Sanarwar Balfour’ da kuma haɗa kai da ‘yan kasuwa sahyoniyawa ta taka gagarumar rawa wajen ƙirƙirar wannan bidi'ar mai suna sahyoniyanci.

A halin yanzu an samar da fagen aiwatar da hakan a aikace. Tun daga waɗancan shekarun a hankali a hankali sun ta harhaɗa ababen da za su kai su ga cimma wannan manufar. Kwatsam kuma bayan Yaƙin Duniya Na Biyu, sakamakon gafala da matsalolin da gwamnatocin yankin suke fuskanta, sai suka bayyanar da maitarsu da kuma sanar da kafuwar haramtacciyar gwamnati maras al’umma ta sahyoniyawa.

Cutarwar wannan ɗanyen aiki a matakin farko ta shafi al’ummar Palasɗinu ne sannan a mataki na gaba kuma ta shafi dukkanin al’ummomin wannan yankin ne.

Dubi cikin abubuwan da suka faru daga baya a yankin nan suna nuni da cewa babbar manufa kana kuma ta kurkusa ta ƙasashen yammaci da masu kuɗin yahudawa wajen samar da gwamnatin sahyoniyawa ita ce samar da wani sansani da zai tabbatar da kasantuwa da kuma ikonsu na dindindin a Yammacin Asiya da kuma samun sauƙin tsoma baki da kuma tabbatar da ikonsu a kan ƙasashe da gwamnatocin yankin. A saboda haka ne suka samar da haramtacciyar ƙasar sahyoniyawa a matsayin tushen tabbatar musu da ƙarfinsu, shin ƙarfi na soji ne ko kuma wanda ba na soji ba, hatta ma suka tsara za su ƙarfafa wannan cutar kansar da makaman ƙare dangi da kuma yadda za su tabbatar da mafarkin da suke da shi na ‘Daga Nilu zuwa Furat’.

Abin baƙin cikin shi ne cewa mafi yawan gwamnatocin larabawa, bayan tsayin dakan da wasunsu suka yi a farko-farkon lamarin, a sannu a hankali sai suka miƙa wuya musamman bayan da ƙasar Amurka ta shigo cikin lamarin. Haka suka yi watsi da nauyin da ke wuyansu na ɗan’adamtaka da Musulunci da siyasa da kuma kishin larabcin da suke da shi, sannan kuma bisa wasu alƙawurra da fata na bogi, suka zamanto masu taimaka wa maƙiya wajen cimma burinsu. Yarjejeniyar Camp David babban misali kana kuma na fili ne na wannan haƙiƙar mai baƙanta rai.

Su ma ƙungiyoyin gwagwarmaya, bayan wasu ‘yan tsayin daka da sadaukarwar da suka yi a shekarun farko-farko, a hankali a hankali sai suka koma ga tafarkin tattaunawar sulhu da ‘yan mamaya da masu goya musu baya, suka yi watsi da tafarkin da zai iya kai su ga cimma manufar Palasɗinu. Tattaunawa da Amurka da sauran gwamnatocin yammaci haka nan da kuma cibiyoyin ƙasa da ƙasa marasa amfani, wani lamari ne da ya faru mai sosa rai kana kuma maras amfani ga Palasɗinawa. Ɗaga itaciyar Zaitun a Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, ba shi da wani sakamako in ba irin hasarar yarjejeniyar Oslo ba da kuma irin makomar Yasser Arafat mai cike da darussa ba.

Bayyanar juyin juya halin Musulunci a ƙasar Iran, ta buɗe wani sabon shafi na gwagwarmayar ‘yanto Palasɗinu. Tun a matakin farko, wato fatattakar jami’an sahyoniyawa da aka yi daga Iran, wanda a zamanin mulkin ɗagutu suna ganin Iran a matsayin ɗaya daga cikin sansanonin tsaronsu, da kuma mai da ofishin jakadancin gwamnatin sahyoniyawa zuwa ga ofishin wakilcin Palasɗinu da kuma katse isar musu da man fetur da sauran manyan ayyuka na siyasa da aka gudanar, dukkanin waɗannan sun taimaka wajen sake rayar da tafarkin gwagwarmaya a dukkanin yankin nan da kuma samar da fatan magance matsalar Palasɗinu a cikin zukatan al’ummomi. Bayyanar ƙungiyoyin gwagwarmaya ta dagula wa gwamnatin sahyoniyawa lissafi – wanda tabbas a nan gaba ma lamarin zai ƙara muni a gare su insha Allah – koda yake ƙoƙarin masu goyon bayan wannan gwamnatin musamman Amurka ma ya ƙaru sosai. Tabbas bayyanar matasa ma’abota imani da sadaukarwa na ƙungiyar Hizbullah a ƙasar Labanon da kuma kafa ƙungiyoyin gwagwarmaya na Hamas da Jihadi Islami a cikin kan iyakokin Palasɗinu, ba wai kawai jagororin sahyoniyawa ba hatta Amurka da sauran azzaluman ƙasashen yammaci ya sanya su cikin damuwa da tsaka mai wuya. Don haka suka shigo da shirin neman ɗauki ta hanyar amfani da wasu Larabawa don ba da kariya da kuma taimakon wannan haramtacciyar gwamnatin ‘yar fashin ƙasa. A halin yanzu ana iya ganin sakamakon irin wannan gagarumin aiki na su cikin mu’amala da maganganun wasu shugabannin gwamnatocin larabawa da kuma wasu maha’intar ‘yan siyasa da masana na ƙasashen larabawa.

A halin yanzu dukkanin ɓangarori biyun suna gudanar da ayyuka mabambanta da nufin faɗa da juna, sai dai da bambancin shi ne cewa sansasanin gwagwarmayar yana ci gaba da samun ƙarfi da kuma kyakkyawan fata. Saɓanin haka, shi kuwa sansanin duhu da kafirci da girman kai a kullum sai koma baya, yanke ƙauna da rauni yake yi. Babban dalilin da ke tabbatar da wannan ikirarin shi ne cewa sojojin sahyoniyawa waɗanda a wani lokaci a baya ake ganinsu a matsayin wasu sojojin gagarabadau da ba a iya samun nasara a kansu sannan kuma cikin ‘yan kwanaki suka samu nasara a kan sojojin wasu manyan ƙasashe guda biyu, amma a halin yanzu sun gaza a gaban dakarun gwagwarmaya ‘yan sa kai a Labanon da Gaza sannan kuma su da kansu suka yarda da cewa sun sha kashi.

Koma dai mene ne, fagen gwagwarmaya fage ne mai tsananin gaske wanda kuma an samu gagarumin sauyi a cikinsa dake buƙatar sanya ido da taka-tsantsan na koda yaushe. Don kuwa batun gwagwarmayar wani batu ne mai muhimmancin gaske kana kuma mai ayyana makoma. Duk wata gafala da riƙon sakainar kashi da kuskuren lissafi da za a yi zai iya zama mai cutarwar gaske.

A saboda haka ina son gabatar da wasu shawarwari ga dukkanin waɗanda suke kishin wannan lamari na Palasɗinu:

1- Gwagwarmayar ‘yanto Palasɗinu, wani jihadi ne saboda Allah kana kuma wani farali ne na Musulunci. Nasara a wannan gwagwarmaya kuwa wani lamari da babu kokwanto cikinsa, don kuwa shi mutum ma’abocin gwagwarmaya koda kuwa an kashe shi ya samu ɗaya daga cikin abubuwa biyu masu kyau ne (ko nasara ko shahada). Bayan hakan, lamarin Palasɗinu wani lamari ne na ‘yan’adamtaka, don kuwa korar miliyoyin mutane daga gidaje da gonaki da matsugunai da wajajen neman abincinsu, shi ɗin ma ta hanyar kisa da ta’adadnci, lamari ne mai sosa lamirin duk wani mutum mai lamiri, sannan kuma matuƙar zai iya to kuwa zai shigo cikin gwagwarmaya da faɗa da wannan ɗanyen aikin. Don haka taƙaita lamarin da cewa wani lamari ne kawai da ya shafi Palasɗinawa, ko kuma larabawa kawai, babban kuskure ne.

Lalle waɗanda suka ɗauki sulhun da wasu Palasɗinawa ko kuma shugabannin wasu ƙasashen larabawa suka yi a matsayin wani lamari da zai magance wannan lamari na Musulunci da kuma ɗan’adamtaka, tabbas sun yi kuskure cikin fahimtar lamarin, a wasu lokutan ma su kan faɗa tarkon ha’inci.

2- Manufar wannan gwagwarmaya ita ce ‘yanto dukkanin ƙasar Palasɗinu – daga Teku zuwa Kogi – da kuma dawowar dukkanin Palasɗinawa ƙasar su ta haihuwa. Tabbatar da hakan ta hanyar kafa wata gwamnati a wani ɓangare na ƙasar, shi ɗin ma ta hanyar wulaƙanci da ke cikin halaye da ɗabi’un sahyoniyawa, hakan ba lamari ne da ke tabbatar da haƙƙoƙi ba kamar yadda kuma ba lamari ne mai tabbatuwa ba. Haƙiƙanin lamarin shi ne cewa a yau miliyoyin Palasɗinawa sun kai wani matsayi na tunani da ƙwarewa da dogaro da kai da za su iya tabbatar da wannan jihadi mai girma, sannan kuma ko shakka babu bisa taimako na Ubangiji za su kai ga nasara, kamar yadda Allah Ya ke faɗin cewa: “Babu shakka Allah zai taimaki mai taimakonSa. Haƙiƙa Allah Mai ƙarfi ne Mabuwayi”…ko shakka babu da dama daga cikin musulmi a duk faɗin duniya za su taimaka musu da kuma kasancewa tare da su, insha Allah.

3- Amfani da duk wata hanya da duk wani ƙarfi na halal wanda shari’a ta yarda da shi a wannan gwagwarmaya, ya halalta ciki kuwa har da goyon baya na ƙasa da ƙasa. Sai dai wajibi ne a nesanci dogaro da gwamnatocin ƙasashen yammaci da kuma cibiyoyin ƙasa da ƙasa a zahiri da baɗini da kuma ‘yan amshin shatansu. Su ɗin nan suna ƙiyayya da duk wani lamari mai tasiri na Musulunci; babu abin da ya dame su da duk wani haƙƙi na ‘yan’adam da na al’ummomi; su ɗin nan su ne ummul aba’isin ɗin hasarori da ayyukan ta’addancin da ke faruwa ga al’ummar musulmi; ya zuwa yanzu wata cibiya ta duniya ce ko kuma wace azzalumar ƙasa ce suka yi wani abu dangane da ta’addanci, kisan gilla, yaƙuƙuwan neman tsokana, ruwan bama-bamai da bala’o’in da aka ƙirƙira da suka faru a wasu ƙasashen musulmi da na larabawa?

A yau duniya tana ƙirga adadin ɗaiɗaikun mutanen da suka rasa rayukansu a duniya sakamakon annobar Korona, amma babu wanda ya tambaya ko kuma yake ƙirga adadin waɗanda suka mutu da kuma wane ne ke da alhakin zubar da jinin dubun dubatan shahidai da fursunonin yaƙi da waɗanda suka ɓace a ƙasashen da Amurka da Turai suka kunna wutar yaƙi? Wane ne alhakin irin waɗannan jinanan da aka zubar ba bisa haƙƙi ba a ƙasashen Afghanistan, Yemen, Libiya, Iraƙi, Siriya da sauran ƙasashen duniya yake wuyansa? Wane ne ke da alhakin irin wannan ɗanyen aiki, fashi, rusau da zaluncin da ke faruwa a Palasɗinu? Me ya sa babu wanda yake ƙirga adadin waɗannan miliyoyin ƙananan yara da mata da maza da ake zalunta a duniyar musulmi? Me ya sa babu wanda yake miƙa saƙon ta’aziyyarsa dangane da kisan gillar da ake yi wa musulmi? Me ya sa miliyoyin Palasɗinawa za su shafe sama da shekaru saba’in a wajen gidaje da ƙasarsu, su ci gaba da rayuwa a matsayin ‘yan gudun hijira? Me ya sa Masallacin Ƙudus mai alfarma, wanda shi ne Alƙiblar musulmi ta farko, zai ci gaba da fuskantar irin wannan keta hurumin? Cibiyar da ake kiran da Majalisar Ɗinkin Duniya ba ta aiki da nuyin da ke wuyanta, haka nan cibiyoyin da ake kiransu da na kare haƙƙoƙin bil’adama sun yi gum da bakunansu. Sannan me ya sa taken da ake rerawa na ‘kare haƙƙoƙin ƙananan yara da mata’ bai haɗawa da ƙananan yara da matan Yemen da Palasɗinu da ake zalunta ba?.

Wannan dai shi ne yanayin ƙasashen da suke tinƙaho da ƙarfi na yammaci da kuma cibiyoyin da suke da alaƙa da su na duniya. Yanayin wasu gwamnatoci ‘yan amshin shatansu na yankin nan ya ma ɗara irin na waɗancan ɗin muni da rashin mutumci …

A don haka wajibi ne al’ummar musulmi ma’abota kishi da riƙo da addini su dogara da kansu da kuma irin ƙarfi na cikin gida da suke da shi; su bayyanar da irin ƙarfin da suke da shi a fili sannan kuma ta hanyar dogaro da Allah su yi ƙoƙarin magance duk wata matsalar da suke fuskanta.

4- Wani lamari mai muhimmanci da bai kamata ƙwararrun ‘yan siyasa da na soji na ƙasashen musulmi su rufe ido kansa ba, shi ne siyasar Amurka da sahyoniyawa wajen haifar da fitina da faɗa cikin sansanin ‘yan gwagwarmaya ba. Haifar da yaƙin basasa a Siriya, killacewa ta soji da kisan kiyashi dare da rana a Yemen, haka nan da ta’addanci, rusau da kuma samar da ƙungiyar Daesh a Iraƙi, da makamantan hakan a wasu ƙasashen na daban na yankin nan, dukkanin waɗannan wani ƙoƙari ne na shagaltar da sansanin gwagwarmaya da kuma taimakon haramtacciyar gwamnatin sahyoniyawa. Wasu ‘yan siyasar ƙasashen musulmi, wasu ba tare da saninsu ba, wasu kuma da saninsu, suna taimakawa wannan makirci na maƙiyan. Hanyar hana aiwatar da wannan baƙar siyasar a mafiya yawan lokuta ta kasance wata buƙata da kuma fata ce ta matasa masu kishi na ƙasashen musulmi. Bai kamata matasan dukkanin ƙasashen musulmi musamman na ƙasashen larabawa su gafala daga wannan kira ta marigayi Imam Khumaini ba da yake cewa: “Duk wani ihu (duk wata ƙiyayya) da kuke da ita, ku tura kan Amurka – koda yake tabbas har da sahyoniyawa ma.

5- Siyasar tabbatar da haramtacciyar ƙasar Isra’ila a yankin nan ɗaya ne daga cikin manyan siyasa da manufar Amurka. Wasu daga cikin gwamnatocin larabawa na yankin nan da suke taka rawar da Amurka take takawa, suna ci gaba da share fagen tabbatuwar hakan ta hanyar ƙulla alaƙa ta tattalin arziki da sauransu. Lalle wannan ƙoƙarin ba zai kai ga gaci ba. Gwamnatin sahyoniyawa cutarwa ce ga yankin nan kuma ko shakka babu za a kawar da ita sannan kuma za ta kasance aibi da kuma kafar zubar da mutumci ga waɗanda suka ba da dukkanin ƙarfinsu wajen biyan buƙatar siyasar ma’abota girman kan. A ƙoƙarin da wasu suke yi wajen halalta wannan mummunan aiki na su suna faɗin cewa gwamnatin sahyoniyawar ta zamanto wata haƙiƙa ce da babu yadda za a iya da ita; alhali sun mance da cewa wajibi ne a yi faɗa da wannan cutar mai cutarwa sannan kuma a kawar da ita daga doron ƙasa. A yau cutar Korona wata haƙiƙa ce amma dukkanin mutane masu lamiri suna ɗaukar faɗa da ita a matsayin wani wajibi da ya kau kansu. Ko shakka babu ƙwayar cutar sahyoniyanci ba za ta ɗore ba sannan kuma bisa himma da ƙoƙari da imani da kishin matasan wannan yankin za a tumɓuke ta.

6- Babbar shawara ta ita ce kira zuwa ga ci gaba da riƙo da tafarkin gwagwarmaya da tabbatar da haɗin gwuiwa da aiki tare tsakanin ƙungiyoyin gwagwarmaya da kuma kara faɗaɗa fagagen jihadi a duk ƙasar Palasɗinu. Wajibi ne kowa ya taimakawa al’ummar Palasɗinu a wannan fagen na jihadi mai tsarki. Wajibi ne kowa ya ƙarfafa waɗannan hannaye na gwagwarmaya na al’ummar Palasɗinu. Mu cikin alfahari muke faɗin cewa duk wani abin da muke da shi za mu ba da shi ga wannan tafarkin. A wani lokaci a baya, mun gano cewa ɗan gwagwarmayar Palasɗinu, yana da addini da kishi da kuma jaruntaka, abin da kawai ya rasa shi ne makami. Bisa taimako da shiriya ta Ubangiji mu ka tsara wani shiri wanda sakamakonsa ne irin ƙarfin da Palasɗinawa suka yi ta yadda a yau Gaza za ta iya tsayin daka wajen tinƙarar wuce gona da irin sahyoniyawa maƙiya sannan kuma ta yi nasara a kansu. Samun irin wannan sauyin a sassan da ake kira da yankunan da aka mamaye lalle zai ƙara kusanto da manufa ta ƙarshe da ake son cimma dangane da lamarin Palasɗinu. Ko shakka gwamnatin cin gashin kan Palastinawa tana da nauyi mai girma a kanta kan wannan lamarin. Ba za a iya magana da irin waɗannan maƙiya marasa tausayi in ba tare da harshe na nuna ƙarfi da tsayin daka ba, alhamdu lillahi akwai wannan yanayi a cikin al’ummar Palasɗinu ma’abota ƙarfi da jaruntaka. A halin yanzu matasan Palasɗinawa suna ƙishirwar kare mutumcinsu. Hamas da Jihadi Islami a Palasɗinu da kuma Hizbullah a Labanon sun yanke wa kowa hujja. Duniya ba ta manta ba kuma ba za ta manta lokacin da sojojin sahyoniyawa suka ƙetare kan iyakan Labanon inda suka kai har zuwa birnin Beirut da kuma lokacin da babban ɗan ta’addan nan mai suna Ariel Sharon ya aiwatar da kisan gillar Sabra da Shatila ba, haka nan kuma ba ta mance ba kuma ba za ta manta wancan lokacin da waɗannan sojojin dai suka ɗebi kashinsu a hannu daga wajen dakarun Hizbullah ta yadda ba su da wata mafita face gudu da kuma amincewa da shan kashi, suka fice daga kan iyakan Labanon suna roƙon a tsaida wuta….wannan shi ake kira da ƙarfi da kuma tsayin daka. Kada ku damu cewa wata ƙasar Turai, wacce za ta ci gaba da zama cikin kunya na har abada sakamakon sayarwa Saddam da makamai masu guba da ta yi, ta haramta ayyukan ƙungiyar Hizbullah ma’abota jihadi da ɗaukaka. (Wata ƙima) Haramcin gwamnati irin Amurka wacce ta samar da ƙungiyar ta’addancin nan ta Daesh da gwamnati irin wancan gwamnatin Turai ɗin da ta yi sanadiyyar mutuwar dubun dubatan mutane a Iran da yankin Halabca na Iraƙi take da ita.

7- Magana ta ƙarshe ita ce ƙasar Palasɗinu ta Palasɗinawa ce, don haka wajibi ne a gudanar da ita daidai da yadda suke so. Gudanar da kuri’ar raba gardama tsakanin dukkanin mabiya addinai da ƙabilun Palasɗinu wanda kusan shekaru ashirin kenan muka gabatar da wannan shawarar, ita ce kawai hanyar kawo ƙarshen wannan matsala ta Palasɗinu. Wannan shawarar tana nuni da rashin ingancin ikirarin ƙyamar yahudawa da mutanen yammaci da kafafen farfagandarsu suke yi (mana). Bisa wannan shawarar, Palasɗinawa, yahudawansu da kiristocinsu da musulmansu, za su fito kafaɗa da kafaɗa wajen kaɗa kuri’ar don zaɓan irin tsarin siyasa da suke son yayi iko a ƙasar Palasɗinu. Abin da ya zama wajibi a kawar da shi shi ne tsarin sahyoniya da kuma sahyoniyanci, wanda wata bidi’a ce cikin koyarwar addinin yahudanci kana kuma baƙo ne a cikin addinin.

Daga ƙarshe ina jinjinawa shahidan Ƙudus kama daga Sheikh Ahmad Yasin da Fathi Shiƙaƙi da Sayyid Abbas Musawi har zuwa ga babban kwamandan Musulunci kana kuma gwarzon gwagwarmaya da ba za a taɓa mantawa da shi ba Shahid Ƙasim Sulaimani da babban mujahidin ƙasar Iraƙi Shahid Abu Mahdi Al-Muhandis da sauran shahidan Ƙudus, sannan kuma ina isar da saƙon gaisuwa da sallama ga ruhin marigayi Imam Khumaini wanda ya buɗe mana wannan tafarki na ɗaukaka da jihadi kamar yadda kuma na ke roƙon gafarar Ubangiji wa babban mujahidi marigayi Husain Sheikh al-Islam wanda shekara da shekaru yayi yana ba da gudummawarsa ga wannan tafarkin.

 

3900728

 

captcha