IQNA

Nakhala Ya Gargadi Masu Ha’inci Dangane Da Batun Quds

23:26 - May 22, 2020
Lambar Labari: 3484824
Tehran (IQNA) shugaban kungiyar Jihadul Islami Ziyad Nakhala ya yi gargadi dangane da ha’incin wasu kasashen larabawa dangane da batun Qds da Falastinu.

Tashar al’alam ta bayar da rahoton cewa, a zantawar da ta yi da babban sakataren kungiyar jihadul Islami Ziyad, ya bayyana cewa, babbar matsalar da ake fuskanta dangane da wasu larabawa da suke hada baki da Isra’ila wajen cutar da al’ummar Falastinu ya fi muni a kan mamaye Falastinu.

Ya ce abin ban takaici ne yadda wasu daga cikin ‘yan uwansu larabawa ne suke yin aiki tare da yahudawa babu dare babu rana wajen cutar da al’ummar Falastinu, tare da halasta wa yahudawa mamayar yankunan muslmi a Falastinu, daga ciki har da masallcin quds mai alfarma.

Kakhala ya ce abin da Iran ta yi dangane da batun ya isa abin alfahari ga dukannin falastinawa da larabawa da ma musulmi baki daya, inda ba ta boye ma duniya ba kan taimakon da take baiwa al’ummar falastinu, kuma ita ce kan gaba wajen kare duk wani abu da ya shafi falastinu a duniya.

Baya ga haka ya kara da cewa, dukkanin matsin lamabar da Iran take fuskanta daga kasashe masu girman kai naduniya da takunkuman da suke kakaba mata, duk hakan sakamako ne na goyon bayan al’ummar Falastinu, da kuma sukar Isra’ila kan zaluncin da take yi kan Falastinawa.f

 

3900808

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iran falastinawa goyon bayan
captcha