IQNA

Musulmin Amurka Sun Raba Taimakon Abinci Ga Mabukata A Ranar Idi

23:50 - May 24, 2020
Lambar Labari: 3484832
Tehran (IQNA) musulmin kasar Amurka a birnin Dearborn na jihar Michigan sun raba abinci kyauta ga mabukata a ranar idi.

Shafin yada labarai na detroit ya bayar da rahoton cewa, a yau Lahadi mabiya addinin musulmi a garin Dearborn na jihar Michigan sun raba abinci kyauta ga mabukata a daidai lokacin da suke idin karamar salla.

Wannan mataki na zuwa da nufin taimaka ma iyalan da suka shiga kuncin rayuwa sakamakon killace jama'a da aka yi saboda hada yaduwar ctar corona.

Mazin Shahab shugaba cibiyar musulmin kasar Amrka ya bayyana cewa, corona ba za ta iya raunana zukatan musulmi kan yin taimako ba, domin kuwa taimakon mabukaci yana daga cikin koyarwar addinin musulunci, ba tare da la'akari da cewa wanda za a taimaka wa musulmi ne ko ba musulmi ba, domin musulunci addini ne na 'yan adamtaka da tausayi da jin kai.

 

3901160

 

captcha