IQNA

Sayyid Nasrullah:

Karfin Da Gungun Masu Gwagwarmaya Ke Samu Ne Dalilin Wanzuwar Amurka A Yankin

23:49 - May 27, 2020
Lambar Labari: 3484840
Tehran (IQNA) babban sakataren kungiyar Hizbollah Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, Amurka tana kara wanzar da kanta ne a yankin gabas ta tsakiya saboda karfin da ‘yan gwagwarmaya ke samu.

Babban sakataren kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon, Sayyid Hassan Nasrallah, ya bayyana cewa Amurka a da ‘yan korenta  ayankin gabas ta tsakiya sun damu matuka da irin karfi da masu gwagwarmaya da zalunci da babakere na ‘yan mulkin suke kara samu a kullum.

Haka nan kuma Sayyid Hassan Nasrallah ya sake yin gargadi game da shirin Isra’ila na mamaye yankunan Falasdinawa na yammacin kogin Jordan.

A cikin hirar da ya yi da gidan rediyon Noor na Lebanon ranar Talata, Sayyid Hassan Nasrallah ya kira gwamnatin Isra'ila a matsayin wata cutar kansa da ba ta da halasci a yankin gabas ta tsakiya, kamar yadda shafin yanar gizon Al Manar TV ya ruwaito.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila t abakin firayi ministanta Benjamin Netanyahu ya yi furuci da cewa, suna da shirin fara mamaye yankunan yammacin Kogin Jordan daga ranar 1 ga watan Yuli mai zuwa.

A cewar Netanyahun, wannan yana daga cikin yarjejeniyar karni, kuma tun a shekara ta 1948 suke jiran damar da za su mamaye yankunan yammacin kogin Jordan, saboda haka yanzu dama ce ta zo, wadda ba za su taba bari ta kubuce musu ba.

A ranar 28 ga watan Janairun farkon wannan shekara ta 2020 ce dai shugaban kasar Amurka Donald Trump, ya sanar da shirinsa na yarjejeniyar karni, tare shelanta birnin Quds a matsayin fadar mulkin Isra’ila.

Wannan shiri dai yana ci gaba da shan kakkausar suka da nuna rashin amincewa daga bangarori daban-daban na duniya, da hakan ya hada da majalisar dinkin duniya, da kuma kungiyar tarayyar turai gami da kungiyar tarayyar Afirka.

 

3901439

 

 

 

captcha