Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, tun a ranar Laraba da ta gabata ce aka bude dukkanin masallatai a kasar Tunisia domin ci gaba da gudanar da salla bayan rufe su na tsawon watanni uku a jere.
Ministan ma'akatar kula da harkokin addini a kasar ya bayyana cewa, dole ne kowane mutumzai zo masallaci ya zo da dardumarsa domin yin salla.
Haka nan kuma ya jaddada cewa, wajibi ne a kiiyaye dukkanin kaidoji da dokoki da jami'an kiwon lafiya suka kafa domin hana kamuwa ko yaduwar cutarcorona, da hakan yahada da saka takunkumin rufe fuska da wanke hannuwa.
a jiya an bayar da rahoton cewa ba a samu mutum ko daya da ya kamu da cutar corona a kasar Tunisia ba, inda adadinin wadanda suka kamu baki daya ya kai 1087, sai kuma 968 sun warke 49 kuma sun rasa rayukansu.