IQNA

Karatun Kur’ani Na Abdulbasit A kasar Pakistan

22:56 - June 07, 2020
Lambar Labari: 3484870
Tehran (IQNA) Abdulbasit Abdulsamad fitaccen makarancin kur’ani dan kasar Masar ya gabatar da karatun kur’ani a kasar Pakistan.

Abdulbasit Muhammad Abdulsamad Salim Dawud, sannnen makarancin kur’ani ne a duniya, wanda ya shahara da kyakkyawan sautinsa na karatun kur’ani, wanda ya kasance shi ne shugaban kungiyar makaranta da mahardata kur’ani na farko a kasar Masar.

An haifi Abdulbasit Abdulsamad a farkon watan Janairun shekara ta 1927 a garin Armenat na kasar Masar, ya kuma rasu a ranar 30 ga watan Nuwamban 1988.

Ya gudanar da karatun surat Waqi’a  a kasar Masar a  shekara ta 1987, wato shekaru 33 da suka gabata, shekara guda kenan kafin rasuwarsa.

3903376

 

 

 

captcha