Shafin yada labarai na Sadal Balad ya bayar da rahoton cewa, El-neny ne ya saka wannan faifan bidiyo da kansa a cikin shafinsa na twitter.
Ya saka karatun kur’ani na Mushar Rashid Alafasi makarancin kur’ani dan kasar Kuwait ne.
Muhammad Elneny wanda ya kasance fitaccen dan wasa dan asalin kasar Masar, ya bayyana cewa a halin yanzu ya dakatar da wasa ne saboda yaduwar cutar corona.