Shafin yada labarai na Al-shuruq News ya bayar da rahoton cewa, a ranar Laraba mai zuwa kasashen musulmi za su gudanar da zaman gaggawa domin tattauna batun shirin Isra’ila na mamaye yankunan Falastinawa da ke yammacin kogin Jordan tare da hade su da sauran yankunan da ta mamaye.
Taron dai zai samu halartar ministocin harkokin waje ne na kasashe mambobi a kungiyar, wanda za a gudanar ta hanyar hotunan bidiyo ta yanar gizo.
A farkon wata mai kamawa ne dai Isra’ila ta sanar da cewa za ta hade yankunan Falastinawa na yammacin Kogin Jordan, wadanda majalsar dinkin dniya ta ayyana su a hukmance a shekara ta 1967 a matsayin yankunan Falastinawa ne da Isra’ila ba ta hakki a cikinsu.