Shafin yada labarai na afrigatenews ya bayar da rahoton cewa, Sheikh Ahmad Muhammad bin Aukal daga yankin Alfujaij mujahidah kasar Libya, ya rubuta kur’ani mai tsarki a cikin shekaru hudu.
Ya rubuta kur’anin bisa ruwayar Qalun bin naïf, kamar yadda kuma ya tsara rubutuna cikin salo mai kayatarwa.
Kwafin kur’ani yana shafuka 621, kamar yadda ya dauki watanni 7 yana kayata shafukansa, haka nan kuam yak an yi alwala duk lokacin da zai yi rubutun.