Shafin yada labarai na almirsad ya bayar da rahoton cewa, wannan babban malamin kur’ani ya kasance har a karshen rayuwarsa yana karatun kur’ani, inda ya rasu yana karatun wasu ayoyi daga cikin surat Anbiya.
Sheikh Abduladi Abduljalil ya kasance a cikin wannan lokacin ne a lokacin da wasu suke daukarsa da bidiyo kamar yadda za a iya gani idan aka matsa hoton bidiyon.