IQNA

Mutanen Cikin Saudiyya Ne Kawai Za Su Aikin Hajjin Bana

23:56 - June 23, 2020
Lambar Labari: 3484922
Tehran (IQNA) Hukumomin Saudiyya sun sanar da cewa, ‘yan kasar da kuma sauran kasashen ketare da suke cikin kasar ne za su gudanar da aikin hajjin bana.

Kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya bayar da rahoton cewa, ma’ikatar kula da ayyukan hajji ta kasar ta sanar da cewa, a shekarar bana ‘yan asalin kasar ta Saudiyya da kuma sauran ‘yan kasashen ketare da suke cikin kasar a halin yanzu ne za su gudanar da aikin hajji a wannan shekara.

Sanarwar ma’aikatar aikin hajji ta saudiyya ta ce, an dauki wanann matakin ne sakamakon bullar cutar corona a wanann shekara, wanda kuma haduwar miliyoyin mutane wuri guda ka iya zama babbar matsala ta yaduwar cutar.

Haka nan kuma bayanin ya yi ishara da cewa, kare rayuka da lafiyar bil adama yana da cikin ayyuka na wajibi a cikin addinin muslunci, a kan haka dole ne a dauki wannan mataki saboda larura.

Kamar yadda kuma bayanin ya tabbatar da cewa, zaa dauki dukkanin matakan da suka dace na kiwon lafiya a yayin gudanar da aikin hajjin na bana.

 

3906343

 

captcha