Shafin yada labarai yaum sabi ya bayar rahoton cewa, an shirya bude wannan sabon masallaci ne a cikin watan Ramadan da ya gabata, amma saboda corona aka dage budewar.
A karon farko an yi kiran salla a cikin masallacin, wanda shi ne masallaci na uku a duniya mafi girma, bayan masallacin Haramin Makka da kuma masallacin ma’aiki (SAW) da ke Madina.
Masallacin yana fadin mita dubu 180, kuma zai iya daukar masallata dubu 120 a lokaci guda, kamar yadda kuma yada wurin ajiye ababen hawa da zai iya daukar motoci dubu 6 a lokaci guda.
Haka nan kuma masallacin yana manyan dakuna taro guda biyu masu fadin mita dubu 16, daya yana da kujeru 1500 a cikinsa, daya kuma 300.
Haka nan kuma akwai dakin karatu mai fadin mita dubu 21 da 800, wanda yake da kujeru 2000 na zama a cikinsa.