IQNA

Mutane Fiye da Dubu 20 Sun Gudanar Da Sallah Juma’a A masallacin Aqsa

22:46 - June 27, 2020
Lambar Labari: 3484932
Tehran (IQNA) fiye da musulmi dubu 20 ne suka gudanar da sallar Juma’a a masallacin Aqsa a wannan Juma’a.

Shafin yada labarai na Arab News ya bayar da rahoton cewa, a jiya Juma’a fiye da musulmi dubu 20 ne suka gudanar ad sallar Juma’a a masallacin Aqsa tare da daukar matakan da suka dace domin kare kai daga kamuwa da cutar corona.

Sheikh Azzam wanda shi ne ya jagoranci sallar Juma’a ya bayyana a cikin huduba cewa, kiyaye ka’idoji da jami’an kiwon lafiya suka bayyana wajibi ne.

Daga cikin hard a zuwa masallaci da darduma, kowa da tasa, haka nan kuma kiyaye tazara tsakanin masallata  a cikin sahu, da kuma yin amfani da takunkumin fuska.

Ya ce a halin yanzu akwai bayanin cewa mutane 72 suka kamu da cuta a cikin birnin Quds, wanda kuma hakan yana a matsayin abin da ke kara wajabta daukar dukkanin matakai domin kariya.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, daga bangaren masu kula da masallacin Aqsa, suna daukar matakai na fiye das aka magunguna masu kashe kwayoyin cuta.

3907038

 

captcha