IQNA

Mambobin Majalisa 30 Sun Bukaci Johson Da Ya Nemi Gafarar Bosniyawa

22:42 - July 11, 2020
Lambar Labari: 3484973
Tehran (IQNA) Wasu daga cikin ‘yan majalisar dokokin kasar Burtaniya sun bukaci Boris Johnson da ya nemi afuwa daga musulmin Bosnia kan furucin da ya yi dangane da kisan da aka yi musu a Srebrenica.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, kimanin ‘yan majalisar dokokin Burtaniya talatin ne tare da wasu fitatun ‘yan siyasa da marubuta na kasar suka aike wa Firai ministan kasar da wasika, inda suka kiraye da ya nemi afuwa daga al’ummar Bosniya kan furucin da ya yi a kan kisan kiyashin da aka yi musu.

A cikin wata makala da ya taba rubuwa a shekara ta 1997, Boris Johson ya bayyana kisan da aka yi wa musulmin Bosnia da cewa, shi ne mafi muni a nahiyar turai bayan yakin duniya na duniya, amma kuma su wadannan musulmin da aka kashe a Bosnia ba mala’iku ba ne.

A cikin makalar Johnson ya yi kokarin bayyana kisan dad aka a yi wa mutane a nahiyar turai a lokacin yakin duniya na biyu da cewa shi ne ya fi muhimmanci a mayar da hankali kansa, fiye da kisan musulmin Bosnia.

Wannan kalami dai ya bakanta ran mutane da dama a ciki da wajen kasar ta Burtaniya, inda  a halin yanzu da aka sake tayar da maganar, ‘yan siyasa da kungiyoyin kare hakkin bil adama suka yi ca a kansa.

3909940

 

 

captcha