IQNA

Zanga-Zanga A London Domin Adawa Da Sayawar Wa Saudiyya da Makamai

22:29 - July 13, 2020
Lambar Labari: 3484982
Tehran (IQNA) daruruwan mutane ne suka gudanar da jerin gwano a  jiya a birnin London domin nuna adawa da sayarwa Saudiyya da makamai da Burtaniya ke yi.

Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a jiya a birnin London daruruwan mutane ne suka gudanar da jerin gwano domin nuna adawa da sayarwa Saudiyya da makamai da Burtaniya ke yi wadanda ake kashe dubban fararen hula da su a Yemen.

Masu gangamin sun tarua  gaban ginin hukumar radio da talabijin ta gwamnatin Burtaniya wato BBC domin isar da sakonsu, daga nan kuma suka nufin babban titin da ke isa zuwa majalisar dokokin kasar.

Babban abin da masu jerin gwanon ke fadi shi ne, babu adalcia  cikin matakin da gwamnatin Burtaiya ta dauka na sayar da makamai na biliyoyin daloli da gwamnatin Saudiyya, alhali tana da masaniya kana bin da za a yi da makaman, shi ne harba su kan al’ummar kasar Yemen tare da kashe mata da kananan yara da tsoffi.

 

3910210

 

captcha