IQNA

Mutuwar Daya Daga Cikin Fitattun Masu Kare Hakkokin Bakaken Fata A Amurka

14:44 - July 19, 2020
Lambar Labari: 3484998
Tehran (IQNA) Daya daga cikin fitattun masu kare hakkokin bakaken fata  a kasar Amurka ya rasu ‘yan makonni bayan kisan George Floyd.

A daidai lokacin da har yanzu ake ci gaba da nuna rashin amincewa da akidar nuna wariya tsakanin al’ummomin Amurka, daya daga cikin jagororin bakaken fata na kasar ya rasu.

John Robert Lewis ya rasu a jiya Asabar bayan fama da rashin lafiya, inda daya daga cikin ‘yan majalisar dokokin kasar Amurka Karen Bass ya bukaci shugaban kasar da ya yi shiru da bakinsa kada ya ce uffan dangane da mutuwar John Lewis.

Dan majalisar dokokin na Amurka ya yi wannan kira ne ga shugaban na Amurka, saboda sanin matsayarsa dangane da Lewis, inda yake sukarsa a lokuta daban-daban, saboda matsayarsa ta kin amincewa da nuna wariya ga bakaken fata a kasar ta Amurka, wanda kan haka ne ya dora masa karan tsana.

Lewis ya kasance daga cikin jagororin bakaken fata da suka jagoranci jerin gwano a fadin kasar Amurka, domin nuan rashin amincewa da wari da ake nuna wa babaken fata a shekara ta 1963, kamar yadda kuma ya yi dan majalisar dokokin kasar Amurka fiye da shekaru talatin.

Sakamakon jajircewa da tsayin dakansa ne ala tilas majalisar dokokin kasar Amurka ta amince da hakkokin bakaken bakaken fata a  kasar, inda aka amince a cikin dokokin kasar kan cewa hakkokinsu daidai suke da kowa.

Bayan gwagwarmaya ta tsawon shekaru fiye da 50, tsohon shugaban Amurka Barack Obama ya ba shi lambar yabo ta farar hula mafi girma ta kasar Amurka a shekara ta 2011.

Duk da gwagwarmayar yaki da nuna wariya da suka yi, amma daga bisani kuma an sake samun bullar wasu masu irin wannan akida, daga ciki kuwa hard a shugaban kasar ta Amurka mai ci a yanzu wanda yake da irin wannan ra’ayi, wanda sakamakon haka ne aka yi wa George Floyd kisan gilla.

Sai dai wannan lamari kuma ya zama masomin fadaka a kasar ta Amurka da ma duniya baki daya, inda a halin yanzu masu nuna kyama ga mutane saboda launin fatarsu su ne abin kyama a duniya har da  acikin kasar ta Amurka.

Mutuwar Daya Daga Cikin Fitattun Masu Kare Hakkokin Bakaken Fata A Amurka

Mutuwar Daya Daga Cikin Fitattun Masu Kare Hakkokin Bakaken Fata A Amurka

Mutuwar Daya Daga Cikin Fitattun Masu Kare Hakkokin Bakaken Fata A Amurka

3911216

 

captcha