IQNA

Sabon Tsarin Koyar Da Kur’ani Ta Hanyar Yanar Gizo A Libya

17:54 - July 20, 2020
Lambar Labari: 3485002
An samar da wani sabon tsarin koyar da kur’ani ta hanyar yanar gizo a kasar Libya wanda kwalejin kur’ani ta birnin Tripoli ta samar.

Shafin yada labarai na Ain Libya ya bayar da rahoton cewa, Uamr Alfaituri Alsuwaihi shugaban kwalejin kur’ani ta birnin Tripoli ya bayyana cewa, sun samar da wanna tsari ne wanda zai taimaka wajen koyar da kur’ani domin amfanin masu bukata.

Ya ce tsarin zai taimaka ma kananan yara musamman ‘yan shekaru da ba su wuce 14 ba, haka nan kuma wadanda suke wajen kasar kamar kasashen turai za su fi amfana da shi.

Wasu daga cikin wadanda suka taimaka wajen samar da tsarin sun bayar da shawara kan yadda za a gudanar da shi cikin sauki.

Haka nan kuma ga wadanda suke bukatar samun Karin bayani kan wannan tsari za su iya ziyartar shafin omar@mafaza.com.

 

 

3911547

 

Abubuwan Da Ya Shafa: sabon tsari libya bayani bukata
captcha