IQNA

Mece ce Manufar Amurka Ta Tsokanar Jirgin Fasinjan Iran A Cikin Sararin Samaniya?

22:34 - July 24, 2020
Lambar Labari: 3485015
Tehran (IQNA) Wasu jiragen akin Amurka sun tsokani jirgin fasinjan Iran a cikin sararin samaniyar kasar Syria a jiya.

A jiya Alhamis ce jiragen yakin Amurka samfurin F-15 guda biyu suka zo kusa da jirgin fasinjan kasar Iran na kamfanin Mahan Air wanda yake kan hanyarsa ta zuwa birnin Beirut na kasar Lebanon, a lokacinda yake ratsawa kan sararin samaniyar kasar Syriya.

Rahoton ya ce jiragen yakin sun yi shawagi kusa jirjin fasinjan har zuwa nisan da bai fiti mita dubu ba. Wannan ya tilastawa jirgin fasinjan yin kasa sosai da sauri, inda hakan hakan ya jawo raunata wasu fasinjoji a cikin jirgin.

Labarin ya kara da cewa duk da haka jirgin fasinjan bai tsaya ba har sai da ya sauka a tashar jiragen sama ta Rafikul Hariri na birnin Beirut.

Tuni dai gwamnatin kasar Iran ta shigar da kara a majalisar dinkin duniya da kuma ofishin jiakadancin swizlan da ke birnin Tehran, wacce take kula da lamuran Amurka a kasar, inda ta ke tuhumar gwamnatin Amurka da ta’addanci kan jirgin fasinja na kasar.

A wani bangaren kuma gwamnatin kasar Amurka ta tabbatar da wannan lamarin ta kuma bayyana cewa ta dauki matakin ne don tunanin cewa jirhin fasinjan na yaki ne, amma da ta tabbatar da cewa na fasinja ne ta nisance shi.

Bayan saukan jirgin dai an kai wadanda suka ji raunka zuwa asbitin Rasulul-Azam(s) da ke birnin Beirut inda aka yi masu jinya.

 

3912241

 

 

captcha