IQNA

An Harhada Wasu Tsoffin Littafan Addinin Muslunci A Kasar Habasha

19:59 - July 27, 2020
Lambar Labari: 3485027
Tehran (IQNA) wani mai bincike a kasar Habasha ya harhada wasu tsoffin littafai na addinin muslunci na tarihi.

Shafin yada labarai na al’ain ya bayar da rahoton cewa, Hassan Muhammad Kawo wani mai bincike ne a kasar Habasha, wanda ya samu damar harhada wasu tsoffin littafai na addinin muslunci da tarihinsu ke komawa zuwa ga karni na 14 miladiyya.

Ya ce ba abin mamaki ba ne idan an samu tsoffin littafai na addinin muslunci a cikin kasar Habasha, domin kuwa ita ce kasa ta farko da musulmi suka nufa a lokacin da suka yi hijira tare da umarnin manzon Allah (SAW) daga Makka.

Baya ga haka kuma wannan ya nuna tsahuwar alaka da ke akwai tsakanin al’ummar wanna kasa da kuma msuilmi, inda yanzu haka akwai tsoffin littafai na addinin muslunci da aka rubuta daruruwan shekaru masu yawa da aka samu a kasar habasha, kuma ana ajiye da su a  babban  dakin ajiye kayan tarihi Bilal Al-Habashi da ke birnin Addis Ababa fadar mulkin kasar.

تهیه مجموعه نسخه‌های خطی کمیاب اسلامی توسط پژوهشگر اتیوپیایی +عکس
 
3912824

captcha