An dai haifi Munshawi ne a cikin shekara ta 1920 a garin Munsha da ke Masar, ya kuma hardace kur’ani tun yana da shekaru 8 a duniya.
Ya tashi a gidan makaranta kur’ani, mahaifinsa shi ne Sadiq Munshawi wanda ya kasance makarancin kur’ani, sai kuma kakansa shi ne Taif Munshawi, da kuma dan uwansa Mahmud sadiq Munshawi, wadanda dukkaninsu fitattun makaranta kur’ani ne.
Muhammad Sadiq Munshawi dai yana da salon karatu irin nasa, wanda ya shahara da shi a duniya, wanda kuma wanda ya yi irinsa to yana kwaikwayonsa ne.