Kamfanin dillancin labaran sputnik ya bayar da rahoton cewa, Fu’ad Guichi Honda fitaccen mai fasahar rubutu dan kasar Japan ya yi rubutun ayoyin kur’ani mai ban sha’awa a kan alluna masu daukar hankali.
Wannan fitaccen mai fasahar rubutu ya shahara a duniya, inda ya karbi kyautuka na kasa da kasa a lokuta da dama, inda ba kawai a rubutu ba, hatta akan zane-zane abubuwa masu ban sha’awa.
Ya koyi rubutun larabci kuma yak ware wajen rubuta shi da salo daban-daban mai ban sha’awa da daukar hankali, inda ba musulmi ko larabawa kawai ba, hatta wadanda larabawa ko musulmi ba suna nuna sha’awarsu a kan rubutunsa.
Ya ce ya tasirantu da addinin muslunci a lokacin day a fara rubuta ayoyin kur’ania akn alluna, wanda kuma wannan tasirin ne yasa ya muslunta, inda a halin yanzu baya ga rubuta ayoyin kur’ani yana kuma iya karanta kur’ani mai tsarki.
A halin yanzu yana daga cikin fitattun masu rubutu a duniyar musulmi da ake nuna rubuce-rubucensa masu shaawa na ayoyin kur’ani da kalmomi na addini a cikin harshen larabci da kuma harshen kasarsa ta Japan.