IQNA

Saudiyya Na Taka Tsantsan Nuna Goyon Bayan Kulla Alaka Da Isra’ila Ba

14:26 - August 20, 2020
Lambar Labari: 3485106
Tehran (IQNA) ministan harkokin wajen kasar Saudiyya ya bayyana cewa kasarsa tana goyon bayan duk wani mataki wanda zai iya kawo zaman lafiya a gabas ta tsakiya.

A ziyarar da ya kai kasar Jamus a jiya, ministan harkokin wajen kasar Saudiyya yarima Faisal Bin Farhan ya bayyana cewa, kasarsa tana goyon bayan duk wani mataki wanda a ganinta zai iya kawo zaman lafiya a gabas ta tsakiya.

A lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a jiya a kasar ta Jamus, dangane da batun kulla alaka tsakanin UAE da gwamnatin yahudawan Isra’ila, ministan harkokin wajen kasar ta Saudiyya ya bayyana cewa, daukar matakai da za su kawo zaman lafiya tsakanin larabawa da Isra’ila yana daga kudirin da larabawan suka dauka a shekarar 2002.

Dangane da yiwuwar kulla alaka ta diflomsiyya tsakanin gwamnatin Saudiyya da kuma gwamnatin yahudawan Isra’ila, Bin Farhan ya bayyana cewa, bisa kudirin 2002 saudiyya za ta iya yin duk abin da ta ga ya dace maslahar yankin gabas ta tsakiya.

Haka nan kuma ya bayyana cewa, Isra’ila ce take kawo matsala ga shirin zaman lafiya  atsakaninta da Falastinawa, ta hanyar kirkiro wasu abubuwan da ba za su kawo daidaito tsakaninta da Falastinawan ba, kamar yunkurinta na mamaye yankunan Falastinawa na yammacin kogin Jordan.

Jaridun Isra’ila da dama a cikin wannan mako sun bayar da rahotannin  cewa, tun a cikin shekarun 1990, akwai alaka ta boye tsakanin sarakunan larabawan yankin tekun fasha da kuma Isra’ila, kuma a cikin wadanann shekarun, su kan hadu su yi ganawa ta sirri da jami’an gwamnatin Isra’ila musamman a cikin kasar Saudiyya da kuma Bahrain.

 

3917686

 

captcha