IQNA

Za A Bude Masallaci Mafi Girma A Nahiyar Afirka

22:21 - August 22, 2020
Lambar Labari: 3485110
Tehran (IQNA) Za a bude masallaci mafi girma  a nahiyar Afirka  akasar Aljeriya a ranar cikar shekaru sattin da kasar ta samu ‘yancin kai.

Shafin yada labarai na arabi jaded ya bayar da rahoton cewa, bayan kwashe tswon shekaru 8 a jere ana gudanar da aikin gina wannan katafaren masallaci, an kammala aikinsa a halin yanzu.

Abdulmajid Tabun shugaban kasar Aljeriya, ya bayyana cewa za a bude wannan masallaci nea  farkon watan Satumba, ranar da kasar ta ke cika shekaru satin da samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka.

Masallacin yana fadin mita dubu 180, kuma zai iya daukar masallata dubu 120 a lokaci guda, kamar yadda kuma yada wurin ajiye ababen hawa da zai iya daukar motoci dubu 6 a lokaci guda.

Haka nan kuma masallacin yana manyan dakuna taro guda biyu masu fadin mita dubu 16, daya yana da kujeru 1500 a cikinsa, daya kuma 300.

Haka nan kuma akwai dakin karatu mai fadin mita dubu 21 da 800, wanda yake da kujeru 2000 na zama a cikinsa.

 

3918054

 

captcha