IQNA

Babban Masallacin Tarihi Na Afirka Ta Kudu Ya Kama Da Wuta

22:40 - August 25, 2020
Lambar Labari: 3485118
Tehran (IQNA) babban masallacin tarihi na kasar Afirka ta kudu ya kama da wuta a daren jiya.

Tashar Akhbar 24 ta bayar da rahoton cewa, a daren jiya ne wata gobara ta tashi a cikin babban masallacin kasar Afirka ta kudu da ke birnin Durban daya daga cikin manyan biranan kasar.

Robert Makinzi shugaban hukumar ‘yan kwana-kwana a birnin ya bayyana cewa, bayan da gobarar ta tashi jami’an kwana-kwana sun yi iyakacin kokarinsu wajen fitar da mutane, da kuma kashe gobarar wadda ta yi babbar barna a masallacin da kuma wasu gine-gine da ke kusa da wurin.

Ya ce duk da cewa an samu asarori masu tarin  yawa, amma abin farin ciki kuma a lokaci guda shi ne babu wani wanda ya rasa ransa sakamakon gobarar.

Faisal Sulaiman daya daga cikin mambobin majalisar musulmin kasar Afirka ta kudu ya bayyana cewa, ba su tsammanin cewa lamarin ya faru ne sakamakon wani aiki na ta’addanci ko barna.

Wanann masallaci an gina shi ne tun shekaru 139 da suka gabata, kuma manyan mutane da dama sun sha kai ziyara a wurin, suka hada irin su Nelson Mandela, Muhammad Ali da kuma Yusuf Islam da dai sauransu.

3918894

 

 

 

 

captcha