Shugaban kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas wanda yake ziyara a kasar Lebanon, ya fada a yau Laraba cewa; Lokacin saukar jirgin saman Isra'ila a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, lokaci ne na bakin ciki mai tattare da kuna.”
Isma’ila Haniyya ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da shugaban Majalisar Dokokin kasar Lebanon, Nabih Berry, inda bangarorin biyu su ka tattauna batun yadda kasashen larabawa su ke kulla alaka da Isra'ila wanda manufarsa take hakkokin al’ummar Palasdinu.
Shugaban kungiyar ta Hamas ya kara da cewa; Mun fitar da bayani na baidaya na dukkanin palasdinawa da muke nuna kin amincewarmu da duk wani yankuri na take hakkokin Falasdinawa, musamman batutuwan da su ka shafi birnin Qudus da kasa da hakkin ‘yan gudun hijira na komawa gida, da ‘yantar da fursunonin daga gidajen kurkukun ‘yan mamaya.”