Shafin yada labaran arabi 21 ya bayyana cewa malaman sun fidda wannan fatawar ne a taron da suka gudanar ta yanar gizo a birnin Doha na kasar Qatar a ranar Lahadin da ta gabata.
Taron wanda kungiyar hadin kan malaman addinin musulunci ta shiya ya sami halattar manya-manyan malaman addini fiye da 200 daga kasashe daban-daban a duniya.
Labarin ya kara da cewa, abubuwan da suke faruwa a kasashen Larabawa a halin yanzu, na maida hulda da HKI, amincewa ne da mamayar wari mafi tsarki ga musulmi, sannan zai bawa HKI damar karasa mamayar da take yiwa Falasdinu da kuma korar sauran Falasdinawa daga kasarsu.
3922041