IQNA

Taron Musulmi Da Kiristoci A Kasar Zimbabwe

23:35 - September 21, 2020
Lambar Labari: 3485205
Tehran (IQNA) an gudanar da zaman taro wanda ya hada musulmi da kirista a kasar Zimbabwe.

Cibiyar yada al’adun musulunci daga kasar Zimbabwe ta bayar da bayanin cewa, an gudanar da zaman taron ne wanda ya hada musulmi da kirista domin yin dubi kan wasu lamurra na zamantakewa, wadanda suka hada dukkanin bangarorin.

Babban abin da zaman taron ya mayar da hankali a kansa shi ne, yadda aka yi ta samun matsaloli a lokacin kulle saboda dakilie yaduwar cutar corona, inda hakan ya yi ta jaza cin zarafin mata musamman.

Dukkanin mabiya addinin biyu sun gatabatar da bayanai da suka shafi matsayin zamantakewa da kuma kare hakkoki na jama’a da hakan ya hada da iyali da sauran jama’a da ake rayuwa tare da su, da kuma yin hakuri da juna a cikin kowane irin yanayi.

Haka nan kuma masu jawabi daga bangaren musulmi da kirista, sun jaddada wajabcin ci gaba da kara kiyaye kyakkyawar alaka ta zamantakewa da fahimtar juna da ke tsakanin musulmi da kirista a kasar.

 

3924349

 

 

 

 

captcha