Mabiya mazhabar ahlul bait suna gudanar da tattakin arbain a cikin da wajen kasar Iraki domin raya ranar ta arbaeen na shahadar limami na uku daga cikin limaman tsira na ahlul bait.
A Najeriya ma mabiya mazhabar Ahlul bait karkashin jagorancin Sheikh Zakzaky suna gudanar da irin wadannan taruka da tattaki, inda a yau a cikin jihar Kano an gudanar da irin wannan tattakin tare da halartar daruruwan jama’a, domin raya wannan rana ta arbaeen.
A daidai lokacin da ranar arbaeen ke karatowa, ana ci gaba da gudanar da tattaki a cikin kasar Iraki daga sassa daban-daban na kasar zuwa birnin Karbala mai alfarma, domin halartar tarukan arbaeen da aka saba gudanarwa a kowace shekara, inda za a gudanar tarukan na wannan shekara a ranar Alhamis mai zuwa.
Rahotanni sun ce miliyoyin mutane ne suke gudanar da tattakin a cikin kasar, duk kuwa da cewa a wannan shekara an dauki kwararan matakai na takaita yawan masu halartar taron, musamman daga kasashen ketare.
Mahukuntan kasar sun bayyana cewa sun dauki matakan ne domin dakile yaduwar ctar corona a tsakanin jama’a, inda hatta wadanda suka tafi wannan ziyara a cikin kasar, an lizimta musu wasu ka’idoji wadanda dole ne su kiyaye su, kamar saka takunkumin fuska, wanke hannu akai-akai, da kuma bayar da tazara.
3927817