IQNA

Yarinya ‘Yar Shekaru 6 Ta Hardace Kur’ani A Yayin Zaman Gida Na Korona A Saudiyya

23:53 - October 16, 2020
Lambar Labari: 3485280
Tehran (IQNA) wata karamar yarinya ‘yar shekaru 6 ta hardace kur’ani mai tsarki a kasar Saudiyya.

Shafin yada labarai na Al-khalij Today ya bayar da rahoton cewa, mahaifiyar yarinyar mai suna Hanin ta bayyana cewa, diyarta ta fara karatun kur’ani tun tana da shekaru uku da haihuwa.

Ta ce ta fara koyar da ita hardar kanan surorin kur’ani mai tsarki, a hankali a hankali kuma tana kara samun ci gaba.

Bayan da cutar corona ta bulla, hakan yasa an rufe makarantu, daga nan kuma sai Hanin ta yi amfani da dama da ta samu na zaman gida, inda ta yi ta yin harda har ta kammala hardace kur’ani baki daya.

Hanin dai tana karatu a wata makarantar kur’ani ta kanan yara mai suna Maknun, inda ake karfafa gwiwar yara wajen koyon karatu da hardar kur’ani mai tsarki.

3929411

 

 

captcha