IQNA

Zanga-Zangar Al’ummar Sudan Kan Kin Amincewa Da Kulla Alaka Da Isra’ila

0:09 - October 25, 2020
Lambar Labari: 3485303
Tehran (IQNA) al’ummar Sudan sun gudanar da zanga-zangogin nuna rashin amincewarsu da kulla alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila.

Dubun dubatan al’ummar kasar Sudan ne suka fito kan titunan kasar don gudanar da zanga-zangogin nuna rashin amincewarsu da matsayar da mahukutan kasar suka dauka na kulla alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila.

Rahotanni daga kasar ta Sudan sun bayyana cewar tun a yammacin jiya ne wasu gungun al’ummar kasar suka fito kan titunan birnin Khartoum, babban birnin kasar don yin Allah wadai da matsayar da masu mulkin kasar suka cimma na kulla alaka ta diplomasiyya da haramtacciyar kasar Isra’ila.

Masu zanga-zangar dai suna rera taken da suka hada da: ‘Ba mu amince da tattaunawa da kuma kulla alaka da Isra’ila ba”, “Ba za mu taba mika kai ko kuma dakatar da goyon bayan Palastinawa ba, muna tare da al’ummar Falastinu” suna rera wadannan taken ne kuwa a daidai lokacin da suke cinna wuta ga tutar haramtacciyar kasar Isra’ilan.

Kafin hakan ma dai babban kawancen manyan kungiyoyi da jam’iyyun siyasa na kasar Sudan, cikin wata sanarwa da suka fitar a yammacin jiyan, sun bukaci mahukuntan kasar da su gaggauta janye duk wani batu na kulla hulda da yahudawan Isra’ila, suna masu bayyana matakin da mahukuntan kasar na rikon kwarya suka dauka na yin gaban kansu wajen kulla hulda da Isra’ila, da cewa hakan abu ne mai matukar hadari, kamar yadda suka ce abin da ma mahukuntan na Sudan suka aikata ya yi hannun riga da manufar al’ummar kasar wadanda suka kawar da gwamnatin da ta gabata, kuma daukar matakin yin ko in kula da bukatun al’ummar Sudan domin gamsar da wasu a wajen kasar, ba abu ne da zai haifar da alhairi ga kasar ba.

A jiya Juma’a din ce dai shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa gwamnatin Sudan da ta haramtacciyar kasar Isra’ila sun amince da su kulla alaka ta diplomasiyya a tsakaninsu. Trump ya ce sun cimma hakan ne cikin wata tattaunawa ta wayar tarho da yayi da Benjamin Netanyahu da na Sudan Abdalla Hamdok inda ya ce a nan gaba kadan za su sanya hannu kan yarjejeniyar a fadar White House.

Kungiyoyin Falastinawa ciki kuwa har da gwamnatin cin gashin kan Falastinun sun yi Allah wadai da wannan mataki da Sudan ta dauka.

 

3930903

 

captcha