IQNA

Gangamin Nuna Goyon Baya Ga Manzon Allah (SAW) A Birnin Quds

20:49 - October 30, 2020
Lambar Labari: 3485322
Tehran (IQNA) an gudanar da gangami a yau a cikin harabar masallacin Asqa domin kare martabar manzon Allah daga cin zarafin da ake yi masa.

Gangami ya gudana ne jim kadan bayan kammala sallar Juma’a a yau, inda dubban masallata suka yi ta rera taken yin tir da Allawadai da cin zarafin manzon Allah da kuma keta alfarmarsa da ake yi a kasar Faransa.

Baya ga haka kuma sun yi tir da matakin gwamnatin kasar Faransa a hukumance kan abin da yake faruwa, inda suke bayyana hakan da cewa shi ne babban ummul haba’isin dukkanin abin da ke faruwa na cin zarafin manzon Allah.

Kamar yadda kuma masu gangamin ke ganin cewa matsayar gwamnatin Faransa ce ta jawo martani daban-daban daga musulmi kan hakan, duk kuwa da cewa irin martanin da wasu suke mayarwa a Faransa na kisan jama’a, musulmi ba su goyon bayan hakan.

Haka nan kuma masu gangamin sun kara jaddada matsayarsu ta yin tir da sarakuna da kuma shugabannin larabawa da suke ta hankoron kulla alaka da yahudawan Isra’ila, ba tare da yin la’akari da hakkokin al’ummar Falastinu da Isra’ila ke zalunta ba.

Gangamin na al’ummar birnin Quds ya zo ne a daidai lokacin da ake gudanar da tarukan maulidin manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa a ko’ina cikin fadin duniya, kamar yadda ya zo kuma daidai da lokacin da masu kiyayya da muslunci suke kara tsananta kiyayyarsu a kan ma'aiki ta hanyar cin zarafinsu da kuma neman tozarta matsayinsa madaukaki.

3932135

 

 

captcha