IQNA

Martani Kan Hare-Haren Ta'addanci A Austria

22:16 - November 03, 2020
Lambar Labari: 3485332
Tehran (IQNA) ana ci gaba da mayar da martani dangane da harin ta'addanci da aka kai jiya a kasar Austria.

Gwamnatin kasar ta Austria ta sanar da cewa an kai harin ta’addanci a tsakiyar birnin vienna a jiya Litinin da marece da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da kuma jikkatar wasu.

Bugu da kari jami’an tsaron kasar sun sanar da bude gagarumin farmaki domin dakile abin da yake faruwa na bude wuta da aka yi.

Ministan harkokin cikin gida na kasar ta Austria Karl Nehammer, ya tabbatar da mutuwar wasu mutane sannan kuma ya kira harin na ta’addanci.

Majiyar ‘yan sandan kasar ta Austria, ta ce adadin wadanda aka kashe sun kai 7, kuma mutane da dama ne su ka kai harin.

Har ila yau, maharani sun yi garkuwa da mutane da dama kamar yadda kafafen watsa labarun kasar su ka ambata.

Shugaban kungiyar Yahudawan kasar ta Austria ya ce; ba su da tabbas ko harin an kai shi ne akan dakin bauta na Yahudawa da ofisoshin da suke kusa da shi.

3933075

 

captcha