IQNA

An Gabatar Da Shirin Gina Masallaci A Kusa Da Burnin Manchester Na Burtaniya

22:47 - November 05, 2020
Lambar Labari: 3485339
Tehran (IQNA) an gabatar da wani shiri na gida babban masallaci a kusa da birnin Manchester na kasar Burtaniya.

Shafin yada labarai na The Bolton News ya bayar da rahoton cewa, kwamitin da ke kula da wani karamin masallaci a garin na shirin sauya wa masallacin wuri da nufin kara fadada girmansa.

Masallacin yana a cikin wani otel ne inda musulmin yankin suke gudanar da harkokinsu na addini, amma daga bisani an yanke shawarar gina wani babban masallaci maimakon wannan, wanda zai lakume kudi da za su kai fan miliyan 3.5.

Za  agina masallacin ne a wani wuri a cikin garin na na Bolton, wanda yake da tazarar kilo mita 16 daga birnin Manchester.

Masallacin zai kunshi babban dakin taro, da kuma makaranta ta yara, inda za su rika koyon ilmomomin addinin muslunci, kamar yadda kuma akwai babban wuri na salla da dakin karatu da kuma wurin taruka na mata.

 

3933383  

 

 

 

 

captcha