IQNA

Faransa: Muna Girmama Dukkanin Addinai Har Da Addinin Musulunci

23:28 - November 08, 2020
Lambar Labari: 3485346
Tehran (IQNA) ministan harkokin wajen kasar Faransa ya bayyana cewa kasarsa tana girmama dukkanin addinai da hakan ya hada har da addinin musulunci.

Tashar RT ta bayar da rahoton cewa, Jean-Yves Le Drian ministan harkokin wajen kasar Faransa a yayin ganawa da manema labarai tare da takwaransa na Masar Samih Shukri ya bayyana cewa; musulmi wani bangare ne na tarihin kasar Faransa da ba za a iya raba su ba.

Ya ce abin da ba su amince da shi ba shi ne ta’addanci da sunan addini, wanda kuma ba za su yi kasa a gwiwa wajen yaki da masu tsatsauran ra’ayi ba.

A wannan Lahadi ce ministan harkokin wajen kasar ta Faransa ya nufi kasar Masar, da nufin shawo kan musulmi da suka yi fushi da Faransa kan zane-zanen batunci ga manzon Allah (SAW) da jaridar kasar ke yi tare da goyon bayan gwamnatin kasar, lamarin da ya harzuka musulmi.

Dangane da kauracewa sayen kayayyakin Faransa da musulmi suke yia kasashe daban-daban, ministan na Faransa ya ce yana ganain hakan ba daidai ba ne, babu abin da zai kara jawowa sai rashin fahimta.

A daya bangaren kuma ya gana da babban malamin cibiyar Azhar Ahmad Tayyib, inda malamin ya jaddada rashin amincewa da goyon bayan da gwamnatin Faransa take bayarwa ga masu zanen batunci a kan ma’aiki da sunan ‘yancin fadar albarkacin baki.

Hakan nan kuma babban malamin na Azhar ya bukaci Faransa da ta daina ambaton Kalmar ta’addancin musulunci, domin kuwa addinin musulunci babu ta’addanci a cikinsa, ko da kuwa an samu ‘yan ta’adda tsiraru a cikin musulmi, wanda kuma a cikin kowane addini akwai bara gurbi, kuma rashin adalci ne ga kowane addini idan a hukunta shi da ayyukan baragurbi daga cikin mabiyansa.

 

3934013

 

captcha