Kamfanin dillancin labaran Africa CGTN ya bayar da rahoton cewa, wani mutum ne da ba a san kowane ba, ya jefa wani abu mai fashewa a cikin wani masallaci a ranar Juma’a da ta gabata.
Wata mata da ta sheda abin da ya faru, ta tabbatarwa kamfanin dillancin labaran AP cewa, a gaban idonta mutumin ya jefa wani abu mai fashewa a lokacin da musulmi suke ibada a cikin masalaci, kuma lamarin ya yi sanadiyyar jikkatar mutane da dama, da hakan ya hada har da konewar jiki.
Ministan tsaron cikin gida a kasar Burkina Faso Ousseni Compaore ya ziyarci masallacin domin ganewa idonsa abin da ya faru, inda ya sha alawashin cewa za a gudanar da binike kan wannan lamari, tare da gano duk wadanda suke da hannu a wannan hari domin hukunta su.
Ana danganta wannan harin ne da masu kiyayya da musulmi a kasar, duk kuwa da cewa kasar Burkina Faso kasa ce da musulmi da kiristoci da ma masu bin addinan gargajiya suke zaune lafiya da juna.
A cikin shekarun baya-bayan kasar ta fara fuskantar matsalolin tsaro sakamakon sadadowar da ‘yan ta’adda suke daga kasar Mali suna kaddamar da hare-hare musamman a yankunan arewacin kasar da ke kusa da iyaka da kasar Mali.