Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana gaggauta gine-ginen da take yi a yankunan Falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan da suka mamaye, kafin sabon shugaban kasar Amurka karbi Iko.
Jaridar Haaretz ta haramtacciyar kasar ta bayyana cewa hukumomin gine-gine da kuma filaye a kasar suna gaggauta bada izinin gina sabbin wurare da kuma gaggauta kammala wadanda aka fara cikin watanni biyu da suka rage na sauya shugabanci a kasar Amurka.
Rahotannin sun kara da cewa akwai tsoron cewa zabebben shugaban kasar Amurka Joe Biden ba zai amince da haramtattun gine-ginen da HKI take yi a wadannan yankunan ba.
Wasu kafafen yada labarai sun bayyana cewa zabebben shugaban kasar yana da hannu a dakatar da gine-ginen gidajen da aka yi a gwamnatin Obama, a lokacin da yake mataimakin shugaban kasa.