IQNA

Iran Ta Karyata Rahoton da Ke Cewa An Kashe Wani Kwanadan Alkaida A Cikin Kasarta

22:33 - November 14, 2020
Lambar Labari: 3485366
Tehran (IQNA) Iran ta yi watsi da rahoton da ke cewa an kashe wani babban kwamandan Al-Qa’ida a cikin kasarta.

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi watsi da kuma musanta rahoton da kafafen watsa labaran Amurka suke yadawa na cewa an kashe wani babban kwamandan kungiyar ta’addanci nan ta Al-Qa’ida a birnin Tehran, babban birnin kasar ta Iran, biyo bayan wani hari da Amurka da Isra’ila suka kai.

Jaridar The New York Times ta Amurka ce ta buga rahoton cewa wasu mahara a kan babur da suke aiki wa Isra’ila sun bindige Abdullah Ahmad Abdullah, wanda aka fi sani da Abu Muhammad Al-Masri, mataimakin shugaban kungiyar Al-Qa’idan, a wani titi na birnin Tehran a watan Augustan da ya gabata.

Jaridar ta ci gaba da cewa wasu jami’an leken asirin Isra’ila da suke aiki bisa goyon bayan Amurka ne suka bindige Al-Masri wanda shi ne ya jagoranci hare-haren da aka kai wa ofisoshin jakadancin Amurka a kasashen Kenya da Tanzaniya a shekarar 1998, har lahira a daya daga cikin titunan birnin Tehran.

Sai dai yayin da yake musanta wannan labarin, kakakin Ma’aikatar harkokin wajen Iran din Saeed Khatibzadeh yace babu gaskiya cikin wannan rahoto na jaridar Amurkan yana mai cewa babu wani jami’in kungiyar ta’addancin ta Al-Qaida da yake zaune a Iran.

Mr. Khatibzadeh ya ci gaba da cewa Al-Qa’ida dai kirkirar Amurka da Isra’ila ne. A lokaci bayan lokaci makiyan al’ummar Iran, Amurka da Isra’ila, a kokarin da suke yi na guje wa danyen aikin da Al-Qaidan ta ke yi suna kokarin jingina kungiyar da Iran wanda hakan babu komai kashin gaskiya cikin hakan.

Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen na Iran dai ya kirayi kafafen watsa labaran Amurkan da kada su bari su fada cikin tarkon farfaganda da labaran karya kan Iran da ‘yan siyasar Amurka suke yadawa.

3935049

 

captcha