IQNA

A Canada An Bude Wani Gini Domin Tunawa Da Kisan Musulmi A Masallacin Quebec

22:15 - December 03, 2020
Lambar Labari: 3485425
Tehran (IQNA) an bude wani gini da aka yi domin tunawa da kisan da aka yi wa musulmi a cikin masallacin Quebec na kasar Canada.

Shafin yada labarai na The Province ya bayar da rahoton cewa, a yau an kaddamar da wani gini na musamman a birnin Quebec na kasar Canada, wanda wani mutum mai ayyukan fasaha mai suna Luce Pelletier ya gina, domin tunawa da musulmin da aka kashe a masallacin birnin.

Magajin garin birnin na Quebec Regis Labeaume ne da kansa ya jagorancin bude wannan wuri, tare da halartar wakilan musulmi na birnin, inda ya bayyana cewa yana fatan abin da ya faru na kisan musulmi a birnin ba zai sake faruwa ba har abada.

Ya ce suna fatan ganin an samu ci gaba da zaman lafiya da ke akwai tsakanin musulmi da ma sauran dukkanin mazauna birnin, inda suke rayuwa tsawon shekaru a tsakaninsu tare da girmama juna, wanda kuma shi ne abin da kowa ke fatan gani.

Shekaru uku da suka gabata a ranar 29 ga watan Janairun 2017 ne wani matashi ya kashe musulmi 6  a cikin masallacin birnin Quebec a lokacin da ake gudanar da sallar Magariba, tare da jikkata wasu da dama, a cikin watan fabrairun 2019 an yanke masa hukuncin daurin rai da rai, duk da cewa bayan shekaru 25 yana da damar daukaka kara bisa sharudda.

3938680

 

 

 

captcha