Shafin yada labarai na arabic 21 ya nakalto daga Kamfanin dillancin labaran Bloomberga na Amurka ya bayar da rahoton cewa, Paul Engelmeier alkalin wata kotu a birnin New York na Amurka, ya bukaci hukumar CIA da ta bayar da cikakken rahoto kan kisan gillar da aka yi wad an jaridar Saudiyya Jamala Khashoggi.
Alkalin ya ce babu bukatar gabatar da wasu dalilai kafin gabar da wannan bukata, domin kuwa hukumar liken asirin Amurka CIA tana da cikakkiyar masaniya kan hakikanin abin da ya faru na kisan gillar da aka yi wa Khashoggi a cikin ofishin jakadanin Saudiyya a Istanbul.
Ya kara da cewa, shugaban kasar Amurka Donald Trump da kansa ya fadi a zantawarsa da tashar talabijin ta Fox News a cikin watan Nuwamban 2018 kan cewa, Amurka tana da hoton bidiyo na kisan Khashoggi.
Alkalin ya ce bisa ikirarin da shugaban Amurka ya yi da kansa, da kuma shugaban hukumar CIA Gina Haspel kan cewa suna cikakkun bayanai kan yadda aka kashe Khashoggi, wannan ya isa hujja kan cewa CIA tana da bayani kana bin da ya faru, kuma kotu na bukatar wadannan bayanai.
A cikin watan Oktoban 2018 ne jami’an tsaron kasar Saudiyya da suka hada har da wasu daga cikin masu tsaron lafiyar Muhammad Bin Salman yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya, suka yi wa Jamal Khashoggi kisan gilla, ta hanyar yi masa gunduwa-gunduwa tare da narkar da namansa da sanadarai na acid.
3940018