IQNA

Jagoran Juyin Iran Ya Ce Babu Makawa Kan Daukar Fansa Dangane Da Kisan Sulaimani

21:48 - December 16, 2020
Lambar Labari: 3485463
Tehran (IQNA) Jagoran juyin juya halin musulunci a Iran Ayatollah sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa, fitar da sojojin Amurka daga yankin gabas ta tsakiya, babban martani ne kan kisan janar Qasem Sulaimani.

Jagoran ya bayyana hakan ne a yau, inda yake tabbatar da cewa, babu makawa Iran za ta mayar da martani kan kisan Qasem Sulaimani a lokaci da kuma wurin da ta ga ya dace domin yin hakan, kamar yadda kuma martanin zai shafi wandanda suka bayar da umarnin yin hakan, da kuma wadanda suka aiwatar.

Dangane da batun janye takunkumai a kan Iran ya ce ba shi da wata matsala kan hakan, idan gwamnatin kasar ta ga akwai hanya mafi sauki  domin aiwatar da hakan, amma bai kamata a amince da yaudarar makiya ba.

Haka nan kuma ya bayyana cewa, yana yin yin kira ga jami’an gwamnatin kasar, su mayar da hankali ne wajen rusa takunkuman da aka drawa kasar, maimakon mayar da hankali wajen neman janye su.

Jagoran juyin juya halin na Iran ya ya kara da cewa, Amurka ta kashe fiye dad ala biliya bakawai domin rusa kasashen Syria da Iraki, amma burinsu bai cika ba har yanzu, kuma ba zai cika ba.

Dangane da kasashen turai uku da suke cikin yarjejeniyar nukiliya tare da Iran, wato Jamus, Burtaniya da Faransa, ya bayyana su da cewa da cewa kasashe ne masu tsabar munafunci da yaudara.

Kafofin yada labarai daban-daban na duniya sun mayar da hankali matuka dangane da wannan jawabi da jagoran juyin juya halin muslucni na kasar ta Iran ya gabatar a yau.

Babban abin da kafofin yada labarai suka fi mayar da hankali a kansa shi ne, maganarsa kan daukar fansa dangane da kisan Qasem Sulaimani, wanda ba a cika jin magana irin wannan daga bakinsa ba.

Tun kafin wannan lokacin dai gwamnatin kasar Iran da ma bangarori na tsaro da suka shafi soja da sauransu, sun sha jaddada cewa, daukar fansa kan kisan Qasem Sulamaini wania bu ne wanda babu makawa a kansa, sai dai Iran din ce take da zabin wuri da lokaci na yin hakan.

Wani abu wanda ya fi daukar hankali a cikin wannan magana shi ne cewa, martanin zai kasance  akan wanda ya bayar da umarni, da kuma wadanda suka aiwatar.

Hukumar leken asirin Amurka da kuma ma’aikatar tsaron kasar dai sun sanar da cewa Trump ne da kansa ya bayar da umarnin kashe Qasem Sulaimani, kamar yadda shi ma Trump din yana tinkaho da hakan.

3941564

 

captcha