IQNA

Sayyid Nasrullah: Qassem Sulaimani Gwarzo Ne Da Tarihi Ba Zai Manta Da Shi Ba

23:28 - January 03, 2021
Lambar Labari: 3485521
Tehran (IQNA) babban sakataren kungiyar Hizbullah ya bayyana Qassem Sulaimani a matsayin gwarzon da tarihi ba zai manta da shi ba.

A cikin wani jawabi wanda ya gabatar a daren yau Lahadi, babban sakataren kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon, dangane da cikar shekara daya da kisan Qassem Sulaimani da Abu Mahdi Almuhandis, Sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa, wadannan gwaraza ne na tarihi.

Ya ce Qassem Sulaimani ya bayar da gagarumar gudunmawa  a bangarori daban-daban wajen taimaka al’ummomi da suke karkashin zalunci a kasashe daban-daban, wanda hakan ba a bu ne da yake boye ga kowa ba a duniya.

Ya e saboda irin wannan jarunta tasa ne da kuma gwagwarmaya da zalunci da taimakon raunana, masu zalunci da suke zaluntar raunana suka dauki matakin ganin bayansa ta hanyar kashe shi.

Dangane da Abu Mahdi Muhandis kuwa, Sayyid Nasrullah ya bayyana shi a matsayin abokin tafiyar Qassem Sulaimani a cikin gwagwarmayarsa, wanda kuma irin gudunmawar da Muhandis ya bayar wajen fatattakar ‘yan ta’adda a cikin Iraki da Syria, da kuma dawo wa wadannan kasashe da tsaronsu, babban lamari ne a cikin tarihin rayuwarsa.

Dangane da halin rashin tabbas da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya a ranakun karshe na mulkin Trump kuwa, Nasrullah ya bayyana cewa, dole ne a kara zama cikin shirin fuskantar kowane irin aikin wawanci da Trump ka iya aikatawa a gabas ta tsakiya kafin ya bar mulkin Amurka.

3945469

 

captcha