IQNA

Farfesa Robert Schmuhl: Kimar Siyasar Amurka Ta Zube Kasa Warwas A Idon Duniya

22:44 - January 10, 2021
Lambar Labari: 3485541
Tehran (IQNA) Robert Schmuhl fitaccen masani kan harkokin siyasar kasa da kasa a kasar Amurka ya bayyana yanayin da siyasar kasar ta samu kanta  a ciki da cewa babban abin kunya ne.

A zantawarsa da kamfanin dillancin labaran iqna, Robert Schmuhl fitaccen masani kan harkokin siyasar kasa da kasa daga jami’ar University of Notre Dame da ke kasar Amurka, ya yi ishara da abin da ya faru a ranar laraba da ta gabata, inda dubban magoya bayan Donald Trump daga jhohi daban-daban na kasar Amurka suka taru a birnin Washington, inda Trump din ya gabatar da jawabi a  gabansu a fadar White House.

A yayin wannan gangami Trump ya tunzura su zuwa ginin Capitol na majalisar dokokin kasar, wanda a ranar ne majalisun guda biyu na dattijai da wakilai suke gudanar da zama domin amincewa da sakamakon zabe, inda suke shirin tabbtar da Joe Biden na jam’iyyar Democrat a hukuamance a  matsayin wanda ya lashe zabe.

Sai dai shi kuma a nasa bangaren Donald Trump yana nan kan bakansa na ikirarin da yake yi na cewa shi ne ya lashe zaben, kuma yake zargin cewa an yi magudi, duk kuwa da cewa dukkanin bincike da aka gudanar kan zargin nasa babu wani abu da ya tabbata a kan hakan.

Wannan zabe na Amurka na wannan lokaci ya zo da abubuwa da dama wadanda suka zubar da kimar Amurka a idon duniya, musamman irin tabargazar da Trump ya tafka a cikin shekaru 4 da ya kwashe yana mulkin Amurka, da kuma babbar tabargazar da ya tafka a lokacin zabe, wadda mafi muni a ciki ita ce tunzura magoya bayansa kan su afka kan  majalisar dokokin Amurka, domin hana fitar da kudirin da zai tabbatar da Biden a matsayin zabababne shugaban kasa.

سیاست در آمریکا به ورزشی خونین تبدیل شده است

Farfesa Robert Schmuhl ya ci gaba da cewa, tun bayan abin da ya faru a ranar Laraba da ta gabata, ana ci gaba da samun ‘yan jam’iyyar Republican da suke juya ma Trump baya, yayin da kuma wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatinsa da suka hada hard a ministoci, suka yi murabus.

Masanin ya ce, baya ga ishara da hakan ke yi dangane da gagarumar matsalar da ke cikin jam’iyyar Republican da rarrabuwar kawuna da ke tsakanin ammbobin jam’iyyar wanda siyasar Trump ta haifar da haka, a lokaci guda kuma hakan yana nuni ne matsalar da siyasa da ma demokradiyyar Amurka take ciki.

 

3946332

 

 

 

 

 

captcha