Kamfanin dillancin labaran Palestine ya bayar da rahoton cewa, Hazem Kasem kakakin kungiyar gwagwarmayar Falastinawa ya bayyana cewa, a halin yanzu Isra’ila ta fara shigar da kayan da yahudawa suke samarwa a cikin yankunan Falastinawa da Isra’ila ta mamaye zuwa kasar hadaddiyar daular larabawa UAE.
Ya ce wannan yana a matsayin karfafa gwaiwar Isra’ila ne domin ci gaba da aikinta na mamaya a kan yankunan Falastinawa, haka nan kuma yana a matsayin halasta mata dukkanin ayyukan barna da cin zalun da take yi ne a kan al’ummar Falastinu.
A ‘yan kwanakin da suka gabata, wani babban jami’in gwamnatin yahudawan Isra’ila ya bayyana cewa, kasuwanci tsakanin Isra’ila da UAE zai kai dala biliyan 4 a cikin shekara.
Daga lokacin da gwamnatin kasar UAE ta rattaba hannu tare da Isra’ila watanni hudu da suka gabata kan kulla hulda a tsakaninsu, ya zuwa yanzu kamfanonin Isra’ila da dama ne suka tare a cikin kasar ta hadadiyar daular larabawa suna gudanar da harkokinsu.