IQNA

An Bayar Da Kyautar Liffatan Addini Gami Da Kwafin Kur’ani Dubu 7 Ga Musulmi Argentina

22:32 - January 25, 2021
Lambar Labari: 3485588
Tehran shugaban cibiyar kula da harkokin addininin muslunci ta kasar Turkiya ya jagoranci raba kyautar littafan addini masu yawa ga musulmin kasar Argentina.

Shafin yada labarai na jaridar Daily Sabah ya bayar da rahoton cewa, shugaban cibiyar kula da harkokin addininin muslunci ta kasar Turkiya, da kuma jakadan kasar a Argentina, sun raba kyautar littafan addini da kwafin kur’ani dubu bakawai a masallacin Al Ahmad da ke babban birnin kasar ta Argentina, wadanda aka buga a cikin harshen Isfaniyanci.

A lokacin da yake gabatar da jawabi a masallacin a lokacin raba wadannan littafai, shugaban cibiyar kula da harkokin addininin muslunci ta kasar Turkiya ya bayyana cewa, wadannan littafai ba su da kima ta kudi, amma suna da kima ta ilimi da ke cikinsu.

Idan ya amfana da abin da ke ciki, to ya samu abin da yafi kudi ko dukiya, domin zai amfanar da shi duniya da lahira, kamar yadda kuma yin aiki da abin da ke cikin wadannan littafai na addini da kur’ani mai tsarki shi ne koyarwar addini ga dukkanin musulmi.

Ya kara da cewa, a halin yanzu akwai irin wadanan littafai da aka buga wadanda ake raba a kasashe daban-daban a cikin harsuna daban-daban, musamman ma kasashen da musulmi sukan fuskanci matsala kafin samun irin wadannan littafai saboda karancinsu.

 

 

https://iqna.ir/fa/news/3949618

 

captcha